Jami’an Ƴansanda Sun yi nasarar Kama Ƴan Fashin Daji Da Masu Garkuwa Da Mutane A Wasu Jihohin Najeriya

Rundunar ƴansandan Nijeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi mambobin ƙungiyar ƴan fashin daji ne da ke kai hare-hare da garkuwa da mutane a wasu jihohin arewacin ƙasar.

An kama mutanen ne a ranar 19 ga Disamba a yankin Komen–Masallaci, da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, a cewar rundunar.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama  Abubakar Usman, wanda aka fi sani da Siddi, wanda aka gani a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta yana rike da makamai da kuɗaɗe. Na biyun kuma shi ne Shehu Mohammed wanda ake kira Gide.
Ƴansandan sun ce a yayin samamen sun kwato babur Honda Ace 125, da kuɗi naira 500,000, da bindigar AK-47 tare da harsasai guda 20.
binciken farko ya nuna cewa mutanen na da alaƙa da wata ƙungiyar ƴan fashin daji da ke aiki a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da Kwara, tare da zargin suna shiga harkokin samar da makamai.
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin suna ba da haɗin kai ga masu bincike, yayin da suka bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa ayyukan tsaro.

 

You might also like
Leave a comment