Jami,an sojin Nigeria sunsha alwashin magance matsalar tsaro dawo da Zaman lafiya a nigeria

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce sojojin ƙasar za su yi duk mai yiwuwa don daƙile ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga a jihar Neja da sauran sassan ƙasar.

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai wasu mahara suka far wa Kasuwan Daji da ke jihar ta Neja, inda suka kashe fiye da mutum 40 tare da yin garkuwa da wasu kafin su ƙona kasuwar.

Laftanar Janar Shu’aib ya ce sojojin ƙasar za su mayar da hankali wajen aiwatar da umarnin shugaban ƙasa na kakkaɓe ayyukan ƴanbindigar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ambato shi yana cewa.

Bayan harin na Neja shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaron ƙasar su yi duk mai yiwuwa don kuɓutar da mutanen da maharan suka sace a lokacin harin.

“Za mu baza jami’an tsaronmu a sassan ƙasar nan domin cimma ƙudurinmu na mayar da Najeriya mai zaman lafiya da bin doka”, in ji shi.

You might also like
Leave a comment