Kotu ta tura Malami da iyalinsa gidan yarin Kuje
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da mai ɗakinsa da kuma ɗansa Abubakar Abdulaziz Malami a gidan yarin Kuje, bayan da suka ƙi amince wa da tuhume-tuhume 16 da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar a kansu.
An gurfanar da su a gaban kotun a ranar Talata, inda suka bayyana ƙin amincewa da zargin da ya shafi safarar kuɗaɗen haramun da mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba.
EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami, ɗansa da Hajia Bashir Asabe, tana zargin su da safarar kuɗaɗe da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7.
A cewar hukumar, ana zargin waɗanda ake tuhuma da amfani da asusun banki da dama tare da kamfanoni a tsawon kusan shekaru goma, domin mallakar kuɗaɗen da ake zargin sun samo su ta hanyoyin da ba su dace da doka ba.