kula da marayu aiki ne dake bukatar hada hannun Al,umma don taimakonsu Khadija Ahmad YUSIF (rufaida)

 

A yammacin wannan rana ta juma’a dake a matsayin 2-01-2026 cibiyar ciyarwa fisabilillahi takai ziyara gidan marayu dake makotaka da asibitin nasarawan jihar Kano 

A ziyarar tasu sun tafiwa da marayu abinci Mai Rai da lafiya da ruwan sha da lemo

A nata jawabin wadda ke a matsayin shugabar cibiyar hajiya rufaida ta bayyana cewa wannan aiki an dauki Shekara biyu anayin wannan aiki ga marayun na kusa da  (makota)

Inda ta Kara da cewa Aikin nasu bai tsaya iya ciyarwa ba suna tallafawa masu karamin karfi hadi da tallafawa a fannin da ya shafi samarda ruwan sha kayan koyo da koyarwa

a jawabin ta na karshe Khadija Ahmad yusif (rufaida) tayi Kira gami da Jan hankalin Al’ummar Annabin tsira dasu kasance masu taimakon marayu na kusa Dana nesa

You might also like
Leave a comment