Kwankwaso ya yiwa Abba fatan samun ƙarin hikima a al’amuransa

Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar ranar haihuwarsa.

A cikin sakon taya murna da Kwankwason ya wallafa a shafinsa na X ya bayyana godiyarsa da darajar shekaru da suka yi tare a harkokin siyasa.

Saƙon taya murnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da tambarwar ficewar Abba daga NNPP zuwa APC.

Kwankwaso ya ce Abba ya taka muhimmiyar rawa a tafiyar siyasar Kano, tun daga lokacin da ya kasance mataimakina na musamman, sannan ya zama kwamishina kafin yanzu ya zama gwamnan jihar Kano.

Jagoran NNPPn ya ce gudunmawar Abba Kabir a fannin ci gaban jihar Kano tana da matuƙar amfani, musamman wajen aiwatar da shirye-shirye da manufofin da suka shafi cigaban al’umma da tattalin arziki.

Kwankwaso ya yi addu’ar “Allah ya ba Abba Kabir ƙarin hikima da lafiya da ƙarfin zuciya da kuma fayyace dalilansa a koyaushe.

 

 

You might also like
Leave a comment