Ma’aikatan jinya a Kaduna sun yi barazanar tsunduma yajin aiki

Ma’aikatan jinya a jihar Kaduna sun yi barazanar tafiya yajin  saboda rashin samun ƙarin girma da suka zargi hukumomin lafiya keyi

Wannan yajin aikin na iya kawo cikas ga ayyukan kiwon lafiya a jihar idan ba a gyara ba.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma na Najeriya (NANNM) ta jihar, kwamared Ishaku Yakubu ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake watsi da ci gaban ma’aikatan jinya.

Ya ce, “Muna fuskantar matsaloli da dama, ciki har da rashin gudanar da tsarin ƙarin girma a ma’aikatar lafiya da wasu hukumominta,” inda ya bayyana cewa hakan yana rage ƙwarin gwiwa da aiki tukuru.

Ya Kuma ƙara da cewa ƙungiyar ba za ta ci gaba da jure jinkirin da ke cutar da ci gaban sana’a da darajar ma’aikatan jinya ba.

You might also like
Leave a comment