Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Yi Umarnin Sake Buda Dokokin Haraji
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta ba da umarnin sake dubawa da yiwa dokar garambawul na haraji guda huɗu a cikin jarin dokar gwamnati, biyo bayan kace-nace da jama’a ke yi kan zargin an yi wasu sauye-sauye bayan an riga an amince da su. Majalisar ta jaddada cewa wannan mataki na gudanarwa ne kawai kuma an yi shi ne don kare mutuncin bayanan majalisar.A cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar Wakilai, Akin Rotimi, ya fitar ranar Juma’a, shugabancin gidajen majalisar biyu sun umarci Akawun Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ya sake buga dokokin tare da bayar da Kwafin Gaskiya (CTCs) na nau’ikan dokokin “waɗanda gidajen majalisar biyu suka amince da su yadda ya kamata.”Wannan umarni ya biyo bayan ƙaruwar sharhi daga jama’a game da amincewa, sa hannun shugaban ƙasa, da kuma buga su a cikin Jaridar Gwamnatin Tarayya. Dokokin sun haɗa da: Dokar Harajin Najeriya ta 2025; Dokar Gudanar da Harajin Najeriya ta 2025; Dokar Hukumar Haraji ta Haɗin Gwiwa ta Najeriya (Kafa ta) ta 2025; da kuma Dokar Hukumar Harajin Najeriya (Kafa ta) ta 2025.A cewar Majalisar Wakilai, damuwar da aka nuna ta shafi “daidaita ƙudirin dokokin da Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka amince da su, takardun da aka aika wa Shugaban Ƙasa don sa hannu, da kuma nau’ikan dokokin da aka buga daga baya a cikin Jaridar Gwamnati