Malamai na shirin tsunduma yajin aiki a Nijar

Gamayyar ƙungiyoyin kwadago na Malamai a Jamhuriyar Nijar, za su fara yajin aiki na kwanaki uku daga gobe laraba, 7 ga watan Janairun, 2026 zuwa Juma’a 9 ga watan.

Wata sanarwa da gamayyar ƙungiyoyin ta fitar, ta koka da halin ko in-kula da rashin mutunta yarjejeniyar da suka saka wa hannu daga ɓangaren gwamnati.

Malaman sun buƙaci gwamnati ta biya su illahirin albashin da suke bin ta, da batun biyan albashin kowane kowane wata kamar yadda yarjajeniyar 2022 ta yi tanadi.

Don haka suka buƙaci gwamnati ta mutunta yarjejeniyar 2025 kan batun ɗaukar malaman aiki na dindindin da batun biyan alawus da albashi ga wasu malamai na dindindin da ke karkashin ƙungiyar.

Malamai na shirin tsunduma yajin aiki a Nija

You might also like
Leave a comment