murka ta sake kama wani jirgin dakn mai a kusa da tekun Venezuela
Rahotonni na cewa dakarun Amurka sun sake kama wani jirgin ruwan dakon mai a kusa da gabar tekun Venezuela.
Wani kamfanin kula da sufurin ruwa ya ce jirgin ya yi yunƙurin bi ta wani wuri da rundunar sojin ruwan Amurka ta killace a yankin Venezuela.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta bayar da rahoton cewa Amurka ta saki ma’aikatan jirgin manta biyu da ta kama ranar Laraba a gaɓar Tekun Atalantika.
A baya Amurka ta ce ma’aikatan jirgin za su fuskanci tuhuma.
Kawo yanzu ba a san adadin sauran ma’aikatan jirgin da kuma ƙasashensu ba.