Mutum 25 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Jigawa

Bayanai daga jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya na cewa mutum 25 ne suka mutu bayan kifewar kwale-kwale a jihar.

Sakataren ƙaramar hukumar Guri, inda lamarin ya faru Alhaji B Jaji Adiyani ya tabbatar wa BBC faruwa lamarin inda ya ce jirgin ya tashi daga garin Adiyani na yankin ƙaramar hukumar Guri zuwa garin Garbi da ke ƙaramar hukumar Nguru a jihar Yobe.

Ya ƙara da cewa jirgin ya kife ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, sakamakon lodin wuce kima da aka yi masa.

”An loda wa jirgin fiye da mutum 40, wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idar abin da ya kamata jirgin ya ɗauka, lamarin da ya tilasta masa kifewar”, in ji shi.

Sakataren ƙaramar hukumar ta Guri ya ce zuwa yanzu an zaƙulo gawar mutum 25 daga cikin ruwan.

”Daga ciki mutum uku ƴan asalin Jigawa ne, sauran kuma ƴan Yobe ne kuma tuni aka wuce da su jiharsu domin yin jana’izarsu”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa baya mutanen da suka mutum masu aikin ceto sun samu nasarar ceto wasu mutanen aƙalla 10 da rayukansu, waɗanda tuni aka garzaya da su babban asibitin Nguru.

A lokuta da dama kifewar kwale-kwale kan haddasa asarar rayuka a Najeriya, wata matsala da masana ke alaƙanta da sakacin hukumomi.

You might also like
Leave a comment