NDLEA Ta Kama Mutane 1,018 a Katsina, Ta Kuma Yi Nasarar Daure Mutane 87 Saboda Safarar Miyagun Kwayoyi

Ta Kama Mutane NDLEA1,018 a Katsina, Ta Kuma Yi Nasarar Daure Mutane 87 Hukumar Yaki da sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Katsina, ta samu nasarar daure manyan masu safarar miyagun kwayoyi guda 87, sannan ta kama wasu mutane 1,018 da ake zargi a shekarar 2025.Kwamandan hukumar na jihar (NC), Isma’il Danmalam, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a birnin Katsina, yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan ayyukan hukumar a shekarar data gabata .Mista Danmalam ya bayyana cewa har yanzu akwai mutane 86 da ake zargi wadanda shari’arsu ke gudana a kotu.Ya kara da cewa, daga cikin mutane 1,018 da aka kama, 992 maza ne, yayin da 26 kuma mata ne.A cewarsa, an kwace sama da tan 2.4 na nau’ikan miyagun kwayoyi daban-daban a cikin shekarar da ake nazari akai.Ya jinjina wa shugaban hukumar na kasa, Buba Marwa, bisa kwarin gwiwar da yake ba wa jami’an hukumar, wanda hakan ya taimaka wajen samun wadannan nasarori.“Wadannan nasarori sun fito fili a cikin ayyukan hukumar ta hanyar amfani da dabarun rage samar da kwayoyi (kinetic) da kuma rage bukatar su (non-kinetic).“Wadannan ayyuka sun kai ga kwace dumbin miyagun kwayoyi, wadanda suka hada da kilogiram 1,667.747 na wiwi (cannabis), kilogiram 12.348 na kwayoyin codeine, da kuma wasu nau’ikan kwayoyin masu nauyin kilogiram 793.66,” in ji shi.Ya bayyana cewa hukumar ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kai da fadakarwa guda 203, wadanda suka isa ga mutane 75,135 a makarantu, al’ummomi, da sauran cibiyoyi.

Ya kuma ce kimanin mutane 451 ne aka ba wa shawarwari (counseling), yayin da aka kwantar da mutane 58 a cibiyar gyaran hali don jinya.“Wannan ya nuna jajircewar NDLEA wajen rigakafi, jinya, da kuma sake mayar da mutane cikin al’umma,” in ji shi.Sai dai ya bayyana cewa duk da wadannan nasarori, hukumar na ci gaba da fuskantar kalubale na kayan aiki da sufuri wadanda ke shafar ingancin ayyukansu.Kwamandan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da su tallafa wa hukumar domin shawo kan kalubalen da take fuskanta don samun sakamako mafi kyau.

Yayin da yake jaddada cewa yaki da miyagun kwayoyi nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, ya yi kira ga al’ummomi da su bayar da hadin kai wajen raba bayanai, fadakarwa, da kuma tsaro na unguwanni domin dorewar wannan yaki.Kwamandan ya yi amfani da wannan dama wajen yi wa wasu daga cikin jami’ai 61 da aka kara wa girma kwanan nan ado da sabbin mukamansu.

You might also like
Leave a comment