Rikicin NNPP: Kotu Ta Tabbatar da Dakatar da Dungurawa Yayin da Abiya Ya Zama Shugaban Jam’iyya na Jiha

Rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ya sake ruruwa yayin da  kotun jihar Kano ta tabbatar da dakatar da shugaban jam’iyyar na jiha, Hashimu Suleiman Dungurawa, daga mazabarsa ta Gargari da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar.Haka zalika, kotun ta hana Dungurawa ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban NNPP na jihar Kano har sai an kammala shari’ar baki daya.

Bayanan Shari’ar  cikin wani kuduri na gaggawa (motion exparte) mai kwanan wata 30 ga Disamba, 2025, wanda Shuaibu Hassan da wasu mutane tara suka shigar a kan Hashimu Suleiman Dungurawa da jam’iyyar NNPP biyo bayan dakatar da shi da aka yi tun farko.

Masu shigar da karar, wadanda su ma mambobi ne na mazabar Gargari a karamar hukumar Dawakin Tofa, sun bukaci kotun da ta amince da matakan ladabtarwa da kuma dakatar da Dungurawa daga jam’iyyar. Wannan ya biyo bayan zarge-zargen:•Cin mutuncin ofis da kuma mutuncin Gwamna Abba Kabir Yusuf.•Haifar da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.•Rashin biyan kudaden gudunmawa na jam’iyya (party dues).Hukuncin Kotu Lauyoyin masu shigar da kara, K. Njidda Esq da S. A. Muhammad Esq, sun kuma gabatar da sammacin neman kotun ta tantance ko matakin da suka dauka a kan Dungurawa ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP.Yayin da take bayar da umarnin dakatarwar na wucin gadi a ranar Juma’a, Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta babbar, kotun jiha mai lamba 13, ta amince da bukatar masu karar kamar yadda suka nema.”Kotun ta tabbatar da cewa Dungurawa ya daina gudanar da ayyukan shugabancin jam’iyyar har sai an kai ga karshen shari’ar.”

You might also like
Leave a comment