Rundunar NSCDC ta Jihar Kano Ta Yi Allah-wadai da Kisan Ma’aikacinta Ta Hanyar Soka Masa Wuka
Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), reshen jihar Kano, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya game da kisan gilla da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka yi wa wani ma,akacin wucin gadi na hukumar, Abdurrauf A. Sheriff, ta hanyar soka masa wuka a Kano.Wannan lamari mai ban takaici ya faru ne a kusa da titin kotun Gyadi-Gyadi yayin da da maai,kacin yake gudanar da aikinsa na halal. Wannan wani babban mataki ne na tashin hankali wanda hukumar ba za ta taba amincewa da shi ba.
Rundunar tana sanar da jama’a cewa an kama mutane hudu da ake zargi tare da makamai masu hadari (kamar zarto, Danbida, da kwayoyi) dangane da kisan, kuma a halin yanzu suna tsare suna taimaka wa jami’an tsaro da bincike, da nufin tabbatar da cewa an yi adalci.
Kwamandan NSCDC na jihar Kano, Kwamanda Mohammed Hassan Agalama, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin, sannan ya sake tabbatar wa jama’a aniyar hukumar na yin aiki tare da sauran jami’an tsaro domin kakkabe bata-gari daga jihar.Ya yi kira ga mambobin jami,an’ da su kwantar da hankulansu sannan su ci gaba da ba wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai akan lokaci.