Rundunar Soji Nigeria tace ta Ceto Ritaya Kanal Daga Hannun Masu Garkuwa a Jihar Filato

Rundunar soji ta musamman  “Operation ENDURING PEACE (OPEP)” ta yi nasarar ceto wani babban jami’in rundunar sojin Najeriya mai ritaya, Kanar Ajanaku (Rtd), bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da shi a karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato.

An sace babban jami’in mai ritaya ne a safiyar ranar 5 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 00:45 na dare a gidansa da ke kishiyar Cocin Salvation Army a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Bassa.Bayan samun kiran gaggawa, dakarun sassa na 1 da na 3 na rundunar Operation ENDURING PEACE suka  bazama tare da bin sawun masu garkuwar ta hanyar da suka bi wajen janyewa ta dajin Wildlife Park.

Dakarun, tare da hadin gwiwar tawagar bin sawu ta hukumar leken asiri ta tsaro (DIA) da kuma dakarun sa-kai na yankin  sun ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceto, inda suka binciko maboyar masu laifi da ake zargi a cikin kogo da duwatsu a cikin yankin baki daya.Daga baya  da misalin karfe 14:00 na rana, masu garkuwar sun tuntubi matar jami’in da aka sace inda suka bukaci kudin fansa har Naira Miliyan Dari Biyu (₦200,000,000.00).Bayan da suka lura da yawan dakarun da ke bin sawunsu da kuma matsin lamba, masu garkuwar sun yi barazanar kashe wanda aka sace idan ba a dakatar da aikin binciken ba.Sakamakon haka, dakarun sunka  sauya salon aiki zuwa na sirri, wanda hakan ya kai ga nasarar ceto Kanar Ajanaku (Rtd) da misalin karfe 17:30 na ranar 5 ga Janairu, 2026, a wajen yankin Rafiki, karamar hukumar Bassa, jihar Filato, ba tare da biyan kudin fansa ba.

You might also like
Leave a comment