Rundunar Soji Tace ta Dakile Wani Harin Yan Bindiga a Wasu Al’ummomin Shanono da ke Kano
Rundunar hadin gwiwa ta JTF ta yi nasarar dakile wani yunkuri na yan bindiga na kutsa kai cikin wasu al’ummomi a karamar hukumar Shanono da ke jihar Kano bayan wata doguwar musayar wuta.
Fadan, wanda ya fara tun daren ranar Alhamis har zuwa safiyar ranar Juma’a, ya faru ne a kauyukan Yankwada, Babanduhu da sauran kauyukan da ke makwabtaka da yankin.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), kakakin rundunar sojin Najeriya a Kano, Manjo Zubair Babatunde, ya bayyana cewa yan bindigar sun yi yunkurin mamaye al’ummomin ne a kan babura yayin da suke harbi ba kakkautawa.
Babatunde ya ce harin na ramuwar gayya ne biyo bayan asarar wasu mayakan yan bindigar da suka yi sakamakon luguden wutar sojoji a wata arangama da aka yi a makon da ya gabata.
A cewarsa, maharan sun farwa kauyukan da abin ya shafa ne da misalin karfe 1:00 na dare, lamarin da ya sanya dakarun soji suka mayar da martani cikin gaggawa.
“An fatattaki yan bindigar yadda ya kamata tare da fatattakar su daga yankin,” in ji shi.
Babatunde ya kara da cewa, kai dauki lokaci da rundunar JTF ta yi ya hana asarar rayuka da kuma barna mai yawa ga dukiyar a al’ummomin da abin ya shafa.
Ya tabbatar wa mazauna yankin kudurin rundunar soji na kare rayuka da dukiyoyinsu, inda ya bukace su da su ci gaba da ba wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai akan lokaci.
Kakakin rundunar sojin ya ce sojoji na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana domin dakile wasu hare-haren da kuma dorewar zaman lafiya a fadin jihar.