Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Kai Hari Kan Sansanonin ‘Yan Bindiga a Zamfara

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta sanar da wata gagarumar nasara a yakin da take yi da ‘yan fashi da makami, inda ta yi nasarar kai hare-hare na sama guda biyu a ranar 28 ga watan Disamba a Turba Hill da sansanin Kachalla Dogo Sule da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa an kaddamar da ayyukan ne bisa sahihan bayanan sirri da aka samu daga majiyoyi daban-daban wadanda suka tabbatar da taruwar manyan shugabannin ‘yan bindiga da muhimman kayayyakin aikinsu a wuraren.Ya bayyana cewa, an kai hare-haren ne da gangan kan sansanonin ‘yan bindiga da aka sani da kai hare-hare a jihar Zamfara da jihohin da ke makwabtaka da ita. Jiragen yakin NAF sun kai hare-hare domin rage karfin fadan ‘yan ta’addan da kuma lalata sansanoninsu da suke amfani da su wajen shiryawa da kai hare-hare kan farar hula da jami’an tsaro.Binciken da aka gudanar bayan kammala aikin ya nuna cewa an lalata maboyar ‘yan bindigar da hanyoyin samar musu da kayayyaki, wanda hakan ya kawo cikas ga ayyukansu.Air Commodore Ejodame ya jaddada cewa ayyukan sun bi ka’idojin aikin rundunar NAF, inda aka ba da fifiko ga tsaron farar hula da kiyaye kwararru a fannin aiki.Rundunar Sojin Saman Najeriya ta sake nanata aniyarta na ci gaba da kai hare-hare ta sama tare da hadin gwiwar dakarun kasa har sai an kawar da ayyukan ‘yan bindiga baki daya a yankin. Kakakin ya bayyana yadda wadannan nasarori suka nuna muhimmancin hare-haren da aka gina kan bayanan sirri da kuma hadin gwiwa mai karfi tsakanin hukumomin tsaro.Ya tabbatar wa mazauna jihar Zamfara da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya cewa rundunar NAF ta himmatu wajen maido da zaman lafiya da tsaro mai dorewa, yayin da yake kira ga al’ummomin yankin da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai akan lokaci domin tallafawa kokarin da ake yi na yaki da masu laifi.

You might also like
Leave a comment