Rundunar ‘Yan Sanda jahar bauchi Ta Tura Manyan Jami’an Tsaro Zuwa Alkaleri

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta bayyana  cewa ta tura dimbin jami’an tsaro tare da ingantattun makamai zuwa al’ummomin da ke fama da matsalar tsaro a Karamar Hukumar Alkaleri domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da kuma hana tabatar da  doka da oda.

 

 

 

 

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda a jihar, Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Bauchi, biyo bayan abin da ya kira sake kunno kai na matsalolin tsaro a garuruwan Gwana, Digare da Kafin Duguri na Karamar Hukumar Alkaleri.

 

 

 

 

Sai dai kakakin rundunar ya kwantar da hankalin mazauna garin Mansur, wadanda aka ruwaito sun tsere daga gidajensu saboda fargabar hare-hare, inda ya ce lamarin yana karkashin kulawa jami,an tsaro.

 

 

 

 

“Duk da wasu abubuwan da suka faru a Gundumar Gwana da ke makwabtaka, garin Mansur bai fuskanci wata matsala ba, kuma babu wani  firgita,” in ji Habib.

 

 

 

“INa tabbatar muku cewa an tura dimbin jami’an tsaro tare da ingantattun makamai domin hana duk wata barazanar tsaro da kuma  doka da oda.

 

 

 

jami’anmu na aiki ba dare ba rana don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan da abin ya shafa,”

 

 

 

 

Habib ya kuma tabbatar wa mazauna Karamar Hukumar Alkaleri cewa ba za a bar wa ‘yan bindiga mafaka ba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro har sai an kawar da bata-gari daga yankin.

 

 

 

 

Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Sani Omolori Aliyu, ya jaddada muhimmancin hadin kan al’umma wajen yaki da rashin tsaro.

 

 

 

 

A cewarsa, Kwamishinan ya bukaci mazauna yankin da su rika bayar da sahihan bayanan sirri cikin gaggawa ga jami’an tsaro tare da kai rahoton duk wani motsi ko bakon mutum ko wani abun   zargi a cikin al’ummominsu.

 

 

 

 

 

Habib ya kara da cewa shugaban rundunar ya tabbatar wa jama’a cewa duk bayanan da aka bayar za a dauke su cikin sirri sosai, tare da karfafa gwiwar al’umma su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba.

You might also like
Leave a comment