Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Jigawa Ta Kama ‘Yan Fashi da Makami, Masu Safarar Miyagun Kwayoyi

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane goma (10) da ake zargi a wurare daban-daban na jihar a wani ɓangare na ƙoƙarinta na inganta tsaron jama’a.A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, Shi’isu Lawan Adam, ya fitar, ya bayar da rahoton kama Haruna Sale da Usman Damina Baushe daga Birnin Kudu, waɗanda ake zargi da hannu a cikin badakalar kuɗin waje (foreign currency scandal), tare da kwato kayayyakin da aka yi amfani da su.Bugu da ƙari, an kama Usaini Abdullahi bisa laifin fashi da makami da abokan aikinsa sun ji wa waɗanda abin ya shafa rauni a ƙauyen Kurusko, a ƙaramar hukumar Malam Madori.Haka kuma, an kama Ibrahim Muhd da Ayuba Idiris, daga unguwar Makara Huta a ƙaramar hukumar Hadejia, saboda lalata wutar lantarki (electric transformer) a ƙauyen Mai Rakumi, Malam Madori.Bayan haka, an kama Abdullahi Muhd Bulama, Yusuf Ahmed, da Mamman Manu Garwa bisa laifin haɗa baki don aikata laifi, fashi da makami, da kuma kisan kai (culpable homicide) bayan sun kai hari tare da yi wa Yusuf Usman da Liman Muhd fashi. Yayin da aynzu ansallami  Liman  daga asibiti, an tabbatar da mutuwar Yusuf.Jami’an ‘yan sanda daga Sassan Kaugama, Gumel, Sara, da Hadejia sun kuma gudanar da samame, wanda ya kai ga kama Murtala Bature na garin Kaugama da Musa Yakubu na yankin Guri. Hukumomi sun kwato kayayyaki daban-daban, ciki har da bindiga ta gida (locally made rifle) da harsasai, tabar wiwi (cannabis), allunan Exol, kwayoyin Tramadol, allunan Diazepam, da kuma kuɗi.Rundunar ta bayyana cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar ayyukan laifuka da kuma kiyaye doka da oda, tare da kira ga jama’a da su ba da bayanan da suka dace kan ayyukan laifuka ta hanyoyin da sukadace

You might also like
Leave a comment