Rundunar ‘yansanda ta kama wadanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane tare da samar wa ‘yan bindiga kayan abinci da sauran kayan tallafi.
Wadanda aka kama sun hada da Abubakar Sindiku mai shekaru 25 da Oliver Okoh mai shekaru 35, inda aka cafke su a yankunan titin Sabo Sango da Ilado bayan wani samame na musamman da sashen yaki da garkuwa da mutane ya gudanar bisa sahihan bayanan sirri.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Jimoh Abayomi, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a Akure, inda ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen na cikin wata kungiyar masu garkuwa da mutane.
Ya kara da cewa sun fara bayar da muhimman bayanai ga masu bincike, yayin da aka kwato wasu babura da kayan da ake amfani da su wajen aikata laifukan.
Wannan na zuwa ne bayan sace wasu ma’aurata a yankin Olaribigba Estate da ke Ilu Abo, inda maharan suka yi musu kwanton bauna a kan hanyarsu ta komawa gida.
Haka kuma mazauna yankin Akure sun nuna damuwa kan karuwar rashin tsaro a yankin, tare da kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen dakile ayyukan ta’addanci da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.