Sabbin yarjejeniya 9 da ASUU ta cimma da gwamnatin Najeriya
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU ta ce sun shiga wata sabuwar yarjejeniya da gwamnati, wadda ta ce idan aka ɗabbaƙa, matsalolin da jami’o’in ƙasar suke fuskanta da dama za su kau.
ASUU ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce waɗannan sababbin matakan da suka aminta, gyara ne kan asalin yarjejeniyar ASUU da gwamnatin ƙasar da aka tsara a 2009, wadda aka daɗe ana taƙaddama a kai.
Sanarwar ta ce, “bayan shekaru muna tattaunawa da fama da gwagwarmayar da muka sha, ASUU ta shiga wasu sabuwar yarjejeniya da gwamnatin tarayya a ranar 23 ga watan Disamba.”
A Najeriya, jami’o’in ƙasar da yajin aiki kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai, inda ake yawan shiga yajin aiki, lamarin da yake sa ɗaliban da ya kamata su kammala karatu a shekara huɗu, sukan haura shekara biyar a wasu lokutan.