SERAP ta Kai Ƙarar Gwamnonin Kotu Kan Kuɗin Tallafin Man Fetur
Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da sa ido kan kashe kuɗaɗen gwamnati, a Najeriya, SERAP, ta shigar da ƙara a gaban kotu kan gwamnonin jihohi 36 da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, bisa gazawarsu wajen yin bayani kan yadda aka kashe kudin tallafin man fetur naira tiriliyan 14 da suka karɓa daga rabon kuɗaɗen FAAC.
Ƙungiyar ta ce gwamnonin sun kasa fayyace ayyukan da suka aiwatar da kuɗin, da kuma rahoton kammala ayyukan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, SERAP ta ce ta shigar da ƙarar ne bayan rahotannin da ke nuna cewa gwamnonin jihohi 36 da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja sun karɓi kuɗaɗe masu yawa daga kwamitin rabon Arzikin kasa wato FAAC a matsayin kuɗin tallafin man fetur tun daga tsakiyar 2023.
Ƙungiyar ta shigar da ƙarar ne a ranar Juma’ar da ta gabata a Kotun Tarayya da ke Legas
Mataimakin daraktan ƙungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare, ya yi wa BBC ƙarin bayani:
Mun ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana. Mun aike da buƙatar bayanai ƙarƙashin dokar samar da bayanai ga gwamnonin jihohi 36 da kuma Ministan Abuja, inda muka gabatar musu da tambayoyi masu sauƙi da ya kamata a ce sun riga sun samar da amsoshinsu a bainar jama’a.”
”Mun riga mun san yawan kuɗaɗen da suka karɓa tsawon lokaci, abin da muke nema kawai shi ne a bayyana yadda aka kashe kuɗin ko an kashe su a ayyuka, mene ne matsayin ayyukan, su wane ne ‘yan kwangilar, da kuma nawa aka kashe a bangaren ilimi da kiwon lafiya da sauransu.
Saboda ba mu samu amsa ga buƙatar bayanan ba ne ya sa muka garzaya kotu, domin dokar FOIA ta ba mu damar yin hakan. Wannan ne dalilin shigar da ƙarar.”
Mataimakin daraktan na SERAP ya kuma bayyana irin tasirin da ƙarar za ta yi ga al’ummar Najeriya:
Tasirinta shi ne ƙarfafa gaskiya da riƙon amana. Dokar sanar da bayanai ta FOIA, wadda ta shafi dukkan jihohi ta wajabta wa gwamnonin su rika bayyana irin waɗannan bayanai tun da wuri.
Shigar da ƙarar kotu za ta sa a tilasta wa waɗannan shugabanni su bayyana wa ‘yan Najeriya yadda suka kashe kuɗaɗen. Wannan wani ɓangare ne na dukiyarmu gaba ɗaya, su yi wa al’ummar jihohinsu da ‘yan Najeriya bayani kan kuɗaɗen da suka karba.