Shohon dan takarar shugaban ƙasa a jam,iyyar lebour party ya soki gwamnatin Tinubu kan fara karɓar haraji ba tare da cikakken bayani ba
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya a Jam’iyyar Labour, Peter Obi kuma jigo a jam’iyyar ADC ya ce babu ƙasar da ke samun cigaban da take buƙata ta hanyar tatsar mutanenta kawai.
Obi ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya wallafa a shafukansa na sadarwa, inda ya ce ƙasashen da ya ziyarta, abin da ya fahimta shi ne suna gudanar da mulki ne ba tare da ɓoye-ɓoye ba.
“Maganar gaskiya ita ce dole gwamnati ta riƙa gudanar da mulki a fili, kuma cikin gaskiya da amana, saboda waɗanda ake mulka ba su cancanci ɓoye-ɓoye da rashin gaskiya ba daga waɗanda suke mulkinsu.”
Ya ce shugabanni na gari ba sa tatsar mutane “domin azurta kansu da wasu tsirarun mutane, suna gina amana ne da haɗin kai da aiki tare, wanda shi ne ginshiƙin cigaba mai ɗorewa. Idan har da gaske ake yi game da haraji, dole ya zama an yi bisa gaskiya da amana da kuma fifita jin daɗi da walwalar ƴan ƙasa da cigaban ƙasar.”
Ya ƙara da cewa dole a bayyana yadda kowane haraji yake, “kamar yadda za a karɓa da amfaninsa wajen ciyar da ƙasa gaba. Idan ba a yi haka ba, zai zama kawai an haifar da ruɗani ne da ƙara wa ƴan ƙasar nauyi.”
A ƙarshe ya ce wannan ne karon farko da aka yi cushe a dokar haraji a Najeriya, “domin ita kanta majalisa ta tabbatar akwai sauyi a dokar, amma duk da haka an buƙaci ƴan ƙasar su fara biyan harajin a haka.”