Shugaba Tinubu Ya Sallami Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami Kayode Egbetokun daga mukaminsa na Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya (IGP).
Wasu  majiyoyi daga cikin Police Service Commission sun tabbatar da faruwar lamarin.

 

 

 

A cewar wata majiya, Egbetokun ya ziyarci Fadar Shugaban Ƙasa da ke Presidential Villa a ranar Litinin, inda aka umurce shi da ya fara shirye-shiryen mika ragamar aiki da takardun hukuma domin sauyin

 

 

Zaman Egbetokun a matsayin IGP ya kasance cike da cece-kuce, ciki har da tsawaita masa wa’adin aiki fiye da shekarun ritaya da dokar ‘yan sanda ta tanada — matakin da ya haifar da muhawara kan yiwuwar saba dokokin aiki. Haka kuma, an yi zargin nuna son kai da fifita wasu wajen karin girma a lokacin jagorancinsa.

 

 

 

Bincike ya nuna an samu karin girma cikin gaggawa da ake zargin ba su bi ka’ida ba, musamman game da Babban Jami’in Ofishinsa, Bukola Yemisi Kuti, wadda masu suka suka ce tana da kusanci na musamman da shi.

 

 

 

 

Wani sabon rikici ya taso bayan rahotanni da suka danganta Naira miliyan 100 daga asusun tsaro na Jihar Anambra State da wani Victor, wanda aka ce ɗansa ne. sun nuna damuwa kan yiwuwar karkatar da kudaden jama’a domin amfanin kai, zargin da ake cewa ya kai ga shari’a.

 

 

 

A halin yanzu, majiyoyi daga cikin rundunar sun nuna cewa ana sa ran za a maye gurbinsa da wani babban jami’i daga Jihar Lagos State.

You might also like
Leave a comment