Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya Taya gwamna abba Kabir yusuf murnar cikarsa shekaru 63 a duniya.
A yau 5 ga watan Janairun shekarar 2026 ne Gwamna Yusuf ke cika shekara 63 da haihuwa.
Shugaban Ƙasa bola Ahmad tinubu ya yaba da gaskiya,da rikon amana da tawali’u da haƙur da Abba Kabir Yusuf yake wajen hidimar al’umma, yana mai cewa waɗannan siffofi sun bayyana a yadda yake tafiyar da mulki a Jihar Kano.
A baya, ya riƙe muƙamin Kwamishinan Ayyuka,da Gidaje da Sufuri daga 2011 zuwa 2015, a lokacin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa mulkin gwamna Yusuf a Kano wadda ke ɗaya daga cikin ginshiƙan siyasa cigaba a Arewa na nuna jajircewa wajen bunƙasa cigaban al’umma, musamman a matakin ƙasa da rage raɗaɗin talakawa, bisa tafarkin akidar marigayi Mallam Aminu Kano.
Acewarsa “Ƙwarewar shugabanci da Gwamna Yusuf ya samu a matsayinsa na kwamishina, inda ya kula da muhimman ma’aikatu, ta taimaka wajen shirya shi don sauye-sauyen gine-gine da ake gani a Kano a yau.
Ya kaddamar da shirye-shiryen sabunta birane, gina gadoji da hanyoyin mota, ciki har da titunan kilomita biyar a kowace ƙaramar hukuma.
Shugaban Ƙasa ya yi wa Gwamnan Kano fatan tsawon rai, lafiya da ƙarin damar ci gaba da jagoranci mai kawo sauyi a jihar