Shugaban hukumar inec: ba za mu ce komai zai tafi daidai ɗari bisa ɗari a zaɓen 2027 ba

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, Joash Amupitan ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa hukumar na da ƙarfin aika sakamakon zaɓe ta na’ura a zaɓen 2027, amma ba zai iya tabbatar da cewa komai zai tafi daidai ɗari bisa ɗari ba.

 

 

 

 

 

Amupitan ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi yayin wani taron jin ra’ayin jama’a, inda ya yi kira ga ‘yan ƙasar da su rage tsammani mai yawa, yana cewa hukumar za ta yi iya ƙoƙarinta wajen gudanar da sahihin zaɓe amma ba za a iya cewa ba za a samu wata matsala ba.

 

 

 

 

 

Ya jaddada cewa “zaɓe ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya, kuma ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a da gaskiya a hukumomi na da matuƙar muhimmanci.”

 

 

 

 

 

 

Shugaban INEC ya ƙara da cewa hukumar na da damar tura sakamakon zaɓe ta na’ura, amma babban ƙalubalen shi ne batun aikawa kai tsaye a lokaci guda.

 

You might also like
Leave a comment