Sojoji sun ceto mutum shida da aka sace a Kajuru Jahar Kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun samu nasarar ceto mutum shida da aka sace a yankin Kajuru/Kujama na jihar Kaduna.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X, sojojin sun gudanar da aikin ceton ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, a matsayin wani ɓangare na manyan jerin ayyukan tsaro da aka tsara a yankunan Chikun, Kajuru, Kachia da Kagarko, ciki har da iyakokin al’ummomin da ke kusa da kan iyakar Kauru.

Sanarwar ta ce aikin ya mayar da hankali ne kan taƙaita ayyukan ‘yan bindiga da masu aikata laifuka a yankunan.

Rundunar ta ce, bayan samun kiran gaggawa kan motsin ‘yan bindiga a kusa da tsaunukan Kasso, sojojin da ke gudanar da aikin share fage a yankin Kujeni suka hanzarta zuwa wurin.

“Da isarsu, sojojin suka yi artabu da ‘yan bindigar, wanda ya tilasta musu tserewa cikin daji inda dakarun suka bi sawunsu nan take, har suka samu nasarar kuɓutar da mutanen shida da aka sace,” in ji sanarwar.

Rundunar ta ce an mika mutanen da aka ceto ga wakilan ƙaramar hukumar Kajuru da majalisar masarautar Kajuru domin mayar da su hannun iyalansu.

You might also like
Leave a comment