Sojoji Sun Yiwa Gungun Ƴan Bindiga Luguden Wuta Yayin da Suke Tserewa Bayan Kai Hari A Kano
Rundunar Soja ta Najeriya ta ce jiragen yaƙinta sun hallaka akalla ’yan bindiga 23 da ke tserewa daga Jihar Kano zuwa mamoyarsu a Katsina, a wani samame na haɗin gwiwa karkashin Operation FANSAN YAMMA.
A cewar rundunar, samamen ya biyo bayan harin da ake zargin ’yan bindiga sun kai a daren 1 ga Janairu zuwa safiyar 2 ga Janairu, 2026, a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa na Jihar Kano.
Dakarun hadin gwiwa da ke Kano sun yi gaggawar daƙile harin tare da yi wa ’yan ta’addan mummunar ɓarna, lamarin da ya tilasta musu guduwa.
Sai dai sojojin sun bi sahunsu har zuwa ƙauyen Karaɗuwa da ke Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da Mai taimaka wa Daraktan Hulda da Jama’a na Brigada ta 3, Major Babatunde Zubairu, ya fitar, an bayyana cewa bayanan leken asiri sun nuna cewa ’yan bindigar suna gudanar da jana’izar abokansu da aka kashe a yankin Ɗan Marke da ke Ƙaramar Hukumar Matazu, lokacin da dakarun sama suka gano motsinsu.
An ci gaba da bibiyar su har sai da suka haɗu da baburansu bayan sun ƙetare kwarin rafi busasshe, inda aka yi musu luguden wuta ta sama.
Rundunar ta ce an hallaka akalla ’yan ta’adda 23, yayin da ake kyautata zaton wasu da dama sun samu raunuka.
Harin ya kuma lalata makamai da kayan aiki da dama na ’yan bindigar.
Kwamandan Birget na 3 ya yaba da jarumtaka da jajircewar dakarun sama da na kasa, yana mai cewa sun nuna bajinta na musamman a fagen yaki.
Rundunar Soja ta tabbatarwa da al’ummar Kano cewa yankin ya ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, tare da ci gaba da sintiri da sa ido a kai a kai.
Ta kuma gode wa jama’a bisa goyon bayan da suke bayarwa a yaƙi da ’yan ta’adda, tare da kira da su ci gaba da samar da bayanai cikin lokaci domin taimaka wa jami’an tsaro wajen dakile ayyukan ta’addanci.