Sojoji sunyi nasarar ceto fasinjojin da aka yi yunƙurin sacewa.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta na 13 Brigade sun samu nasarar ceto fasinjoji 18, ciki har da jarirai 2, daga wani jirgin ruwa da ‘yan fashin ruwa suka kama a ranar 11 ga Janairu, 2026.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan fashin ruwa wadanda suka yi amfani da ƙananan jiragen ruwa masu gudu sun kai wa jirgin wanda ke tafe daga Najeriya zuwa Kamaru hari a gaɓar tashar kamun kifi ta Kombo a kogunan Kamaru
Sojoji sun samu kiran gaggawa kan lamarin inda suka yi saurin ɗaukar mataki suka bi ‘yan fashin abin da ya haifar da musayar wuta wanda ya sa ɗaya daga cikin jiragen ƴan fashin ya kife.
Sakamakon haka, ‘yan fashin suka tsere zuwa cikin koguna suka bar fasinjojin inda daga bisani sojojin suka ceto su cikin ƙoshin lafiya.
Kwamandan 13 Brigade na rundunar, Brigadiya Janar PO Alimikhena, ya yaba wa sojojin bisa jajircewa da kwarewarsu a aikin ceton inda ya ce; “Za mu ci gaba da tabbatar da tsaron yankunan da muke aiki da su da kuma kare ‘yan kasa daga duk wani laifi.”
Ya kuma bukaci al’umma da su taimaka wajen bayar da bayanai masu amfani ga sojojin don yaƙi da laifuka a kogunan Cross River da kewaye inda ya jaddada cewa haɗin kai da al’umma na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro.