Sojojin amurka sun Kai Hari Kan Yan,ta,adda a Sokoto
Sojojin Amurka sun tabbatar da cewa sun kai hare-hare kan mayakan kungiyar ISIS a jihar Sakkwato a daren Alhamis, bayan gwamnatin Najeriya ta nemi taimakon hakan.
Ma’aikatar Tsaro ta Amurka ta ce “an kashe ’yan ta’addan ISIS da dama” a wannan aikin da aka gudanar a jiya alhamis, wanda aka tsara tare da gwamnatin Najeriya.
sanarwar tafito me daga sashen rundunar Amurka da ke kula da Afirka India tace: “A bisa bukatar hukumomin Najeriya, sojojin Amurka sun kai hari a jihar Sokoto, inda suka kashe ’yan ta’addan ISIS da dama.”
Harin na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan tashin hankali da hare-haren ta’addanci a arewa maso yammacin Najeriya
Mazauna kauyen Jabo da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar ta Sakkwato dai sun tabbatar da kai hare-haren na Amurka a kusa da kauyen nasu, kodayake sun ce zuwa yanzu babu rahoton mutuwa ko ma jikkata.