Sojojin Najeriya 9 sun mutu bayan taka nakiya a jihar Borno

Rahotannin da jami’an tsaron Najeriya suka fitar, sun ce aƙalla sojoji tara ne suka mutu lokacin da jerin gwanon motocinsu suka taka wani abin fashewa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Wasu sojojin da dama kuma sun jikkata a harin da ya afku a ranar Lahadi.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

Sai dai lamarin ya faru ne a yankin da masu iƙirarin jihadi na ISWAP ke gudanar da ayyukansu da kuma kai munanan hare-hare

You might also like
Leave a comment