Tinubu ya bukaci Yan Nigeria dasuyi haƙuri zasuga alfanun sabuwar dokar haraji

Shugaba Tinubu na Najeriya ya ce idan ƴan Najeriya suka yi haƙuri za a samu yi rayuwa mai inganci ta hanyar alkilta arziƙin ƙasa yadda ya kamata abin da zai sa ƙasar ta yi fice a duniya a wannan sabuwar shekara ta 2026.

Tinubu ya shaida hakan ne a saƙon sabuwar shekara da ya fitar ranar Alhamis inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa ci gaba da gini a kan abin da ta fara na sauye-sauye masu alkairi ga ƴan Najeriya.

“Duk da irin ƙalubalen da duniya ke fuskanta ta fuskar tattalin arziƙi, mun samu gagarumar nasara a 2025 musamman a fannin tattalin arziƙi”.

Dangane  da sabuwar dokar haraji da ta fara aiki, Tinubu ya nemi ƴan Najeriya da su ƙara hakuri domin nan gaba kaɗa za su ga alkairin tsarin.

Ya kuma ce ɗaya daga cikin daillin aiwatar da wannan sabon tsarin harajin shi ne kawo sauyi wajen tatsar ƴan Najeriya harajin da ya wuce ƙima.

“Muna kuma son kawo ƙarshen biyan haraji da yawa inda dukkan matakan gwamnati kan kari haraji. Na yaba wa jihohin da suka amince da shiga tsarin harajin na bai ɗaya domin sauwaƙe wa jama’a yawan haraje-haraje a kan al’umma da kayan abinci.”

“Sabuwar shekarar ta fara da aiwatar da sauye-sauyen harajin da aka yi domin dasa harsashin Najeriya mai adalci da kuma ƙarfi a fannin kudaɗen shiga,” in ji Tinubu.

Idan muka yi haƙuri za mu ga alfanun sabuwar dokar haraji – Tinubu

You might also like
Leave a comment