Tsohon dan takarar mataimakin shugaban Ƙasa a jam,iyyar LP- Datti Baba-Ahmed yace tun yana Nysc atiku ke tsayawa takarar.

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP a Najeriya, Datti Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da za a bai wa sabbin jini dama a siyasar Najeriya.

Cikin wani bidiyon hirarsa da gidan Talbijin na Channels a ƙasar, Datti ya ce tun lokacin da yake yi wa ƙasa hidima (NYSC) Atiku Abubakar ke faman tsayawa takarar shugabancin ƙasa.

”Haka aka zo shekarar 2018 muka shiga zaɓen fitar da gwani tare da shi, haka ma a 2023 muka sake tsayawa takara da shi lokacin ni a matsayin mataimakin shugaban ƙasa”, in ji shi.

”Kuma saboda Allah a sake yin haka a 2027?, akwai buƙatar bai wa sabbin jini damar gwada tasu sa’ar”, kamar yadda ya bayyana.

Datti Baba-Ahmed ya ce akwai matasa sabbin jini masu zummar kawo gyara a siyasar ƙasar, amma yadda aka sanya tsarin zama mai wahala da tsauri na yi musu tarnaƙi.

You might also like
Leave a comment