Tsohon ministan tsaron Nigeria badaru Abubakar ya musanta zargin chanja sheka daga jam,iyar APC zuwa ADC
Tsohon Ministan Tsaro na Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sheka daga jam’iyyarsa ta APC mai mulkin kasar zuwa jam’iyyar hamayya ta ADC.
A wata sanarwa da tsohon ministan ya sanya wa hannu da kansa, ya ce wannan zancen, labarin kanzon kurege ne, kuma wani yunkuri ne kawai na bata masa suna, da kuma kassara harkar siyasarsa.
A tattaunawarsa da BBC wani hadimin tsohon ministan, Kwamared Abba Malami, ya ce su wannan labari ya zo musu ne ma da mamaki:
”Na farko dai babu kanshin gaskiya a cikin wannan magana kuma ta zo mana da mamaki kwarai da gaske.