Wani gini ya rufta yayi sadiyar muwar uwa da ya,yanta huɗu -maidguri

Aƙalla mutum biyar ne suka mutu, ciki har da wata uwa da yara huɗu bayan rugujewar wani gini a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a unguwar Binta Suga da ke birnin Maiduguri, inda ya jefa mazauna yankin cikin jimami.

Wani mazaunin unguwar mai suna Babagana Usman ya shaida wa BBC cewa ginin ba shi da wani lahani kafin ruftawarsa.

“Mutane na wucewa kan hanya gefen wani gida kwatsam sai gidan ya faɗi a kansu. Bayan faɗuwar ginin sai muka ji wata ƙara inda nan da nan muka fito don kawo ɗauki. Mun cire mutum kusan shida a ƙarkashin ɓaraguzan ginin.

“Mutum biyar ne suka mutu sannan ɗaya na karɓar kulawa a asibiti,” in ji Babagana.

Ya ƙara da cewa tuni aka yi jana’izarsu a safiyar yau Litinin.

Mahaifin yara biyu cikin waɗanda suka rasu, Usman Abdullahi, ya ce sun shaku sosai da yaransa.

“Babban wanda ya rasu mai suna Abdulmalik shekararsa 11, sai mabiyinsa wanda suka kasance ƴan uwa. Abin da zan riƙa tunawa da su shi ne karanta al-Qur’ani duk lokacin da suka dawo daga Sallah,” in ji

You might also like
Leave a comment