Wani Hatsarin Mota Ya yi Sanadiyar Mutuwar Ma’aikatan NTA Guda Shida

Rahotanni na cewa akalla ma’aikatan gidan Talabijin na Kasa NTA a jihar Gombe guda shida ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata, sakamakon hatsarin mota da ya faru a Jihar Gombe.

Wadanda suka rasu sun hada da Manu Haruna Kwami, Manajan Gudanarwa da Zarah Umar, Manajar sashen Labarai; da Isa,wanda ya kasance Edita; da Musa Tabra, wanda ya kasance tsohon Manajan Labarai;da Aminu, shi kuma shine direba; da Adams, ma’aikacin Startimes.

Rahotanni sun bayyana cewa Emmanuel Akila (Manajan Labarai),da Jonathan Bara (Manajan Talla), da Steven Doddo (Babban Jami’in Talla) sun samu munanan raunuka kuma suna karbar kulawar likitoci a wani asibi.

You might also like
Leave a comment