Wasu fusatantu Mutane sun kai Hari ofishin civil defence Sun kashe mutum uku

Rundunar Tsaro da Jami’an Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC), reshen jihar Kano, ta bayyana cewa wasu fusatattun jama’a sun kai hari ofishinta da ke Danmaje a Karamar Hukumar Dawakin Kudu, inda suka kashe wasu mutane uku da ake zargi tare da kona ofishin kurmus.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Kano.

A cewar Abdullahi, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na daren Lahadi, 28 ga Disamba, 2025, lokacin da mazauna yankin Yansango suka kawo wasu mutane uku da ba a tantance ko su wanene ba, wadanda ake zargi da satar babura zuwa ofishin NSCDC na Danmaje.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wani wuri da aka sani da aikata fashin babura a yankin.

Ya kara da cewa kafin a fara gudanar da bincike, mazauna garuruwa daban-daban da suka hada da Yansango, Madinawa, Gagarawa, Limawa, Yankatsari, Danmaje da Gurjiya, sun taru a ofishin tare da bukatar a mika musu wadanda ake zargin.

Lamarin ya da yajawo cikin kankanin lokaci  fusatattun mutanen suka kewaye ofishin.

Kafin jami’an agaji su iso, mutanen sun yi amfani da karfi suka shiga ofishin, suka cinna masa wuta sannan suka kashe wadanda ake zargin su uku,

“Jami’anmu da ke bakin aiki sun tsira, sai dai guda uku daga cikinsu sun samu raunuka daban-daban, kuma yanzu haka suna karbar magani,” injishi

Hukumar ta NSCDC ta yi kira ga mazauna Dawakin Kudu da sauran jama’a da su kwantar da hankulansu sannan su guji daukar doka a hannunsu.

Abdullahi ya bayyana cewa Kwamandan rundunar na jihar, Mohammed Hassan-Agalama, bisa umarnin Kwamanda-Janar, ya kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Ya ce ana ci gaba da kokarin gano tare da kamo wadanda ke da hannu a harin domin gurfanar da su gaban shari’a, yayin da ya jaddada kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

You might also like
Leave a comment