Wasu matasa sunyi yunkurin kwacewa Wani kwamandan vigilante babur mai kafa biyu a kauyen Yan kusa-kumbotso

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma daƙile shaye-shayen kayan maye, ta Anti-Phone Snaching a Kano, ta kama wasu matasa biyar da ake zarginsu da da amfani da makamai ga wani kwamandan Bijilante  tare da yunƙurin ƙwace masa Babur mai ƙafa biyu a yankin Ƴan Kusa karamar hukumar kumbotso.

Mai magana da yawun rundunar ta Anti-Phone Snaching , Ibrahim Garba Ahmad, shine  ya tabbatar da Hakan Ga gidan radio  Dala FM Kano, ankama matasane a ranar Laraba 7 ga Janairu, 2026.

Ya kuma ce, sun kama matasan biyar ne biyo bayan kiran gaggawa da su ka samu akan faruwar lamarin, na yunkurin ƙwacewa kwamandan bijilanten Baburin nasa a yankin na Ƴan Kusa.

A cewar sa, “Binciken farko da mu ka fara ya gano mana cewa, a lokacin da lamarin ya faru matasan sun sha kayan maye bayan da su ka fita daga cikin hayyacinsu su ka tare kwamandan Bijilanten riƙe da muggan makamai inda su ka yi yunƙurin ƙwace masa baburin, in ji shi.”

Saidai  daga baya matasan da aka kama basuwuce  shekaru  19, 22, 25, ba, sun bayyana cewa, sun yi yunkurin ƙwace wa kwamandan Bijilante Babur ɗin ne biyo bayan shaye-shayen da su ka yi, amma matasan sunce  sunyi nadamar abunda suka aikata.

kakakin rundunar ta Anti Phone Snaching Kano Ibrahim Garba, ya kuma ce, yanzu haka Kwamdandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya bada umarnin a faɗaɗa bincike a kan matasan, tare da miƙa su wurin da ya dace, domin ɗaukar mataki na gaba.

 

You might also like
Leave a comment