Wasu Tubabbun ‘Fulanin Daji’ Sun Afka wa Ɗan Uwansu a Kasuwar Batsari Saboda wata dadandiyar Gaba.

Lamarin ya faru ne a gaban wakilan Katsina Times, inda maharan suka tarar da Manin Tururuwa a kasuwar sayar da dabbobi, sannan suka shiga saran sa da adda tare da duka da sanduna da itatuwa.

Bayan tabbatar da cewa Manin Tururuwa ya fita hayyacinsa, maharan suka bar shi kwance cikin jini, a halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Daga bisani, bayan da jama’a suka watse, jami’an ‘yan sanda sun iso wajen suka ɗauki Manin Tururuwa zuwa Asibitin Batsari domin samun kulawar gaggawa.

Mani Tururuwa, wanda dan asalin Illela ne a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, sanannen tsohon ɗan bindiga ne da ya amshi shirin sulhu tare da ajiye makamai a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Aminu Bello Masari.

 

Bayan tubansa, ya koma Katsina inda ya rungumi sana’ar saye da sayar da dabbobi. Sai dai a wani lokaci an ce ya sake ɗaukar makami yana fafatawa da wasu ‘yan bindiga da ba su amince da sulhun gwamnati ba.

 

Wani mutum mai suna Saidu Dan Tashshi, wanda ya yi yunƙurin ceton Mani, shi ma ya samu munanan raunuka bayan da aka dukeshi da sanduna. Rahotanni sun ce Saidu yana auren ‘yar uwar Mani Tururuwa.

 

Majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa harin da aka kai wa Mani Tururuwa na da nasaba da ɗaukar fansa kan tsohuwar gaba da ta haɗa su da wasu daga cikin tsofaffin ‘yan bindiga.

 

Wasu Tubabbun ‘Fulanin Daji’ Sun Afka wa Ɗan Uwansu a Kasuwar Batsari Saboda Tsohuwar Gaba

You might also like
Leave a comment