Wasu Yan jam,iyar APC na neman Nyesom Wike ya ajiye muƙamin Ministan Abuja

Zazzafar cacar-baka ta kaure tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, da Sakataren Jam’iyyar APC, Ajibola Bashiru, lamarin da ya kai ga Sakataren jam’iyyar kiran da Wike ya sauka daga muƙaminsa na minista, bisa hujjar cewa ba ɗan jam’iyyar APC ba ne.

Wannan dai na zuwa ne bayan Wike ya gargadi Sakataren da ya tsame hannunsa daga siyasar jihar Ribas, sakamakon sanarwar da shugabancin APC suka fitar cewa Gwamna Siminalayi Fubara ne jagora kuma shugaban jam’iyyar mai mulki a jihar.

Rikicin ya faro ne tun bayan ziyarar da Sakataren APC da tawagarsa suka kai wa Gwamna Siminalayi Fubara a jihar Ribas, inda daga bisani Bashiru ya sake jaddada tsarin jam’iyyar cewa kowane gwam

You might also like
Leave a comment