Wasu yara hudu sun nutse a ruwa a jahar edo

Yara biyu sun mutu yayin da wasu biyu suka tsira bayan sun nutse a wani wurin tara ruwan ambaliya da ke titin Erediauwa, kusa da Sapele Road, a ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha ta Jihar Edo.

 

 

 

 

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, kamar yadda wata majiya ta shadawa Jaridar Punch

 

 

 

 

Wani shaidar gani da ido, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa yara huɗu ne suka je wasa a kusa da wurin da gwamnatin jihar ta ware domin tara ruwan ambaliya.

 

 

 

A cewarsa, yayin da suke wasa ne suka zame suka fada cikin ruwan da ke cike da laka, lamarin da ya janyo

 

 

 

An ce an zakulo gawarwakin yaran biyu daga cikin ruwan, yayin da aka garzaya da sauran biyun zuwa wani asibiti da ke kusa domin kula da lafiyarsu.

 

 

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo, Eno Ikoedem, ta tabbatar da faruwar lamarin.

 

 

 

 

Ta ce an tura jami’an ceto nan take bayan samun rahoton aukuwar lamarin, inda aka tabbatar da mutuwar yara biyun a wurin da abin ya faru.

 

 

 

 

Har ya zudai   ba a sami wani  karin bayani kan halin da sauran yaran biyu da aka ceto suke ciki ba.

You might also like
Leave a comment