Yan Majalisar jahar Rivers Sun Yi Allah wadai da albazaranci da kudin gwamnatin jahar rivers bayan da gwamna ya Tura musu amatsayi Kyautar Kirsimeti.

Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta yi watsi da wata “kyautar Kirsimeti” ta naira 100,000 da aka tura wa asusun banki na ‘yan majalisar bisa umarnin Gwamna Siminalayi Fubara, inda suka bayyana hakan a matsayin abin da ba su nema ba kuma ya saba wa doka.A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, wadda Shugaban Kwamitin Majalisar kan Yada  Labarai, Koke-koke da Korafe-korafe, Enemi George ya sanya wa hannu,

‘yan majalisar sun bayyana cewa dole ne kudaden gwamnati su bi hanyoyin da suka dace, ciki har da amincewar majalisa.Sanarwar, mai taken “Maida Naira 100,000 da Aka Tura wa Asusun ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers Ba Tare da Nema ko Amincewa ba Daga Gwamnan Jihar Rivers”, ta nuna cewa an mayar da kudaden nan take.”A yau, 30 ga Disamba, 2025, mambobin Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta 10 sun sami sakon tura kudi na naira 100,000 kowannensu. An tura wannan kudi ne ba tare da nema ko amincewa ba bisa umarnin gwamna,” in ji sanarw

George ya zargi gwamnan da ci gaba da dibar kudi daga asusun kudaden shiga na jihar ba tare da amincewar majalisa ba tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2023, wanda hakan ya saba wa hukuncin Kotun Koli da Kundin Tsarin Mulki.Ya kara da cewa: “Muna sane da ma’aikatan da ke hada baki da gwamna don saba wa kundin tsarin mulki da dokokin Jihar Rivers. Ayyukansu sun saba wa doka. Muna tabbatar wa mutanen kirki na Jihar Rivers cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukanmu na tsarin mulki.”Sabanin haka, ma’aikatan gwamnati a jihar sun sami irin wannan garabasar Kirsimeti bayan bin hanyoyin amincewa na yau da kullun, wanda hakan ya nuna damuwar Majalisar cewa tura kudin ga ‘yan majalisar ya kauce wa hanyoyin da suka dace.Majalisar ta dage zamanta har zuwa ranar 26 ga Janairu, 2026.

Gwamna Fubara har yanzu bai gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2026 ba ko kuma mika sunayen mutanen da za a nada a matsayin kwamishinoni. Yana gudanar da mulki ne tun bayan dawowarsa daga dakatarwa tare da kwamishinoni takwas kacal wadanda hukuncin Kotun Koli da ya amince da Martin Amaewhule a matsayin Shugaban Majalisa.

 

You might also like
Leave a comment