Yan majalissar Jahar rivers sun zargi wasu manya da hana yunkurin tsige fubara

Majalisar Dokokin jihar Rivers ta yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki na ƙoƙarin yin amfani da kotu wajen neman toshe ƙofar tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

 

A cewar majalisar, yunkurin neman umarni daga babbar kotun jihar da ke wajen birnin Fatakwal na nuni da ƙoƙarin dakatar da yunƙurin tsige shi.

 

Shugabannin majalisar sun jaddada cewa tsarin tsige gwamnan yana tafiya ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ba za su bari wani matsin lamba ko tsoma bakin waje ya hana su sauke nauyin da doka ta ɗora musu ba.

 

Sun kuma ce duk wanda ke da ƙorafi ya bi hanyoyin doka da oda, yayin da suke tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da bin doka wajen gudanar da dukkan matakan da suka shafi batun tsige gwamnan.

 

‘Yan majalisar na neman tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa kan zargin rashin ɗa’a da nuna reni ga majalisar da umarnin kotun koli.

You might also like
Leave a comment