Yan Sandan Kano Sun Kama Mutane Sama da 3,000 Kan Manyan Laifuka a 2025
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cewa ta kama mutane 3,081 da ake zargi da aikata manyan laifuka daban-daban a faɗin jihar daga Janairu zuwa 30 ga Disamba 2025.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan ne a jawabin ƙarshen shekara da ya gabatar a shelkwatar rundunar da ke Bompai, inda ya ce laifukan da aka fi samu sun haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane, dillancin miyagun ƙwayoyi, satar motoci da babura, sata, zamba da kuma harkar daba.
A cewarsa, rundunar ta kama mutum 2,350 da ake zargi da daba kaɗai, tare da kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma kwato makamai, miyagun ƙwayoyi da dukiyoyin sata iri daban-daban.
Bakori ya ce an samu nasarar ne sakamakon ƙarfafa sintiri, amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, tare da ƙaddamar da Operation Kukan Kura, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da waɗannan tsare-tsare a shekarar 2026