Yanzu-yanzu: ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 6 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara shida sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP mai mulki zuwa Jam’iyyar APC, inda suka ce, rikicin cikin gida, shugabancin jam’iyya da kuma rashin kyakkyawan shugabanci a jihar ne ya tilasta musu barin Jam’iyyar.

‘Yan Majalisar sun sanar da sauya shekarsu a hukumance a cikin wasiku daban-daban amma masu kama da juna da aka aika wa Kakakin Majalisar kuma LEADERSHIP ta samu a ranar Alhamis.
Masu sauya shekar su ne Hon. Bashar Aliyu Gummi (Yankin Gummi I), Hon. Nasiru Abdullahi Maru (Maru ta Arewa), Barista Bashir Abubakar Masama (Bukkuyum ta Arewa), Hon. Bashir Bello (Bungudu ta yamma), Hon. Amiru Ahmad Keta (Tsafe ta yamma), da Hon. Muktar Nasir Kaura (Kaura ta Arewa).

You might also like
Leave a comment