Zaftarewar ƙasa ta kashe mutum 18 a DR Congo
Zaftarewar ƙasa ta rutsa da wani ɓangare na ƙauyen Burutsi da ke yankin Kashebere na gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, inda aƙalla mutum 18 suka rasa rayukansu a lardin North Kivu.
A halin da ake ciki, ana gudanar da aikin ceto domin gano waɗanda abin ya rutsa da su.
Zaftarewar ƙasar ta faru ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a ranar Talata yayin da mazauna yankin ke barci.
Gidaje da dama sun ruguje inda rufin ƙarfe na kan wasu gidade ne kawai ake iya gani a wasu wurare.
Wani jami’in yankin ya ce laka mai kauri da duwatsu na kawo cikas ga aikin ceto, yayin da ake kula da waɗanda sukia jikkata a cibiyar kiwon lafiya dake kusa.
Haka kuma mazauna suna tono tarkace domin ceto waɗanda suka tsira ko kuma su gano gawawwaki.
Zaftarewar ƙsar ta katse babbar hanyar zuwa babban birnin lardin, Goma yayin da yankin tsaunukan gabashin DRC ke fuskantar haɗarin zaftarewar ƙasa musamman a lokacin damina.