zargin laifukan zaɓe a Abuja EFCC ta kama mutum 20
Hukumar EFCC ta sanar da kama mutum 20 da ake zargi da aikata laifukan zaɓe yayin zaɓen ƙananan hukumomin babban birnin tarayya, Abuja da aka gudanar a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.
EFCC. Ta ce ta kama su ne a wurare daban daban saboda zarge zargen sayen ƙuri’u da sayar da ƙuri’u da kuma hana jami’ai aiki, inda aka gano kuɗi har Naira miliyan 17,218,700.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar, an ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin da Naira miliyan 13,500,000 a cikin mota da aka ajiye kusa da rumfar zaɓe a yankin Kwali.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kama mutane biyu a Abaji, tara a Gwagwalada, huɗu a Kuje, sannan sauran huɗun a Kwali.
Hukumar ta ce za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Hukumar INEC ce ta gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a dukkan yankuna shida na FCT.
EFCC ta jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido domin tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan matakan zaɓe.