Zargin Makircin EFCC da ICPC Kan ‘Yan Hamayya Ba Gaskiya Ba Ne – Muhammad idress
Gwamnatin Tarayya ta karyata ikirarin da ke yawo a yanar gizo na cewa tana shirin kama mambobin jam’iyyun hamayya suna tsare su, ko kuma gurfanar da su ba bisa ka’ida ba, inda ta bayyana zargin a matsayin na karya da yaudarar jama’a.
Gwamnatin ta mayar da martani ne ga wata takarda da ke zargin kafa wata runduna ta hadin gwiwa tsakanin hukumomi daban-daban a karkashin wani shiri mai suna “ADP4VIP” (Arrest, Detain, Prosecute for Very Important Persons – Kamawa tare da Gurfanar da Manyan Mutane), wanda aka ce an yi shi ne domin nufin manyan ‘yan siyasar hamayya.
A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Talata, gwamnatin ta ce takardar kirkira ce kawai kuma ba ta da wani tushe a zahiri.”
Gwamnatin Tarayyar Najeriya tana bayyana karara cewa ba ta da wani shiri na kamawa ko tsarewa, ko gurfanar da ‘yan hamayya ba bisa ka’ida ba,
Ministan ya jaddada cewa “babu wani shiri mai suna ‘ADP4VIP’,” yana mai kara da cewa zargin wani bangare ne na gangamin yada labaran karya da gangan. Ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali ne kan shugabanci maimakon ramuwar gayya ta siyasa.
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana tsaye daram kuma tana samun nasara wajen aiwatar da muhimman kudurorinta: aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da murkushe rashin tsaro, fadada damar kasuwanci, da kuma dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari,” in
Haka kuma gwamnatin ta zargi wasu mambobin jam’iyyun hamayya da kokarin nuna matakan tabbatar da gaskiya da adalci a matsayin cin zarafin siyasa.