Zelensky ya gana da wakilin Trump kan sabuwar daftarin tsagaita wuta a Ukraine
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ya yi wata doguwar tattauna da Steve Witkoff, wakilin Trump na musamman da kuma surukinsa Jared Kushner kan yadda za a kawo karshen yaki da Rasha.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram, Mr Zelensky ya bayyana tattaunawar a matsayin mai ma’ana inda ya ce sun tattauna wasu sabbin manufofi.
Tun da farko rundunar sojin Ukraine ta ce ta kai wa daya daga cikin matatun man Rasha harin makami mai linzami a yankin Rostov da ke kusa da kan iyaka da Ukraine.
Ta ce matatar ce ke ba motocin yaki na sojojin Rasha mai a yankin gabashin Ukraine da Rasha ta mamaye