Gwamna Fubara Ya Rushe Majalisar Zartarwa ta Jihar Rivers
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya rushe Majalisar Zartarwa ta jihar nan take.
An sanar da rushewar ne a ranar Alhamis.
An kuma umurci dukkan kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da su mika ragamar aiki ga sakatarorin dindindin ko manyan jami’an da suka fi kowa matsayi a ma’aikatunsu.
Gwamna Fubara ya gode wa tsofaffin mambobin Majalisar Zartarwar bisa gudunmawar da suka bayar wajen hidimtawa jihar, tare da yi musu fatan alheri a nan gaba.
An bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Onwuka Nzeshi, ya fitar a ranar Alhamis.