Jiragen sojojin ruwan Amurka sun yi tawo mugama da juna a kusa da Kudancin Amurka
Rundunar sojin Amurka da ke yankin kudancin Amurka ta tabbatar wa BBC cewa wani jirgin ruwan yaƙin sojin ruwan Amurka ya yi karo da wani jirgin ruwan da ke samar da man fetur a lokacin da suke aikin samar da mai.
An bayar da rahoton cewa mutane biyu sun ji ƙananan raunuka yayin aikin da suke gudanarwa a teku kuma \a halin yanzu suna samu kula a asibiti in ji rundunar sojin.
Jiragen ruwan biyu duk sun ci gaba gudanar da ayyukansu a cikin tekun bayan aukuwar lamarin.
Rundunar dai ba ta bayyana abin da ya haddasa hatsarin ba, kuma ta ce a halin yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin.